Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da gidan ruwa na hadin guiwa tsakanin gwamnatinsa da  gwamnatin tarayya da babban bankin duniya wanda zai rika samar da galan 450,000 a kowane yini a  unguwar Bado da Kasarwa a birnin Sakkwato.

Gwamnan a jawabinsa a yau Laraba ya ce a lokacin da suka zagaya a yekuwar babban zaben 2019 sun fahimci al’ummar wannan  yankin na fama da matsalar ruwa kan haka suka kudurci share masu hawayensu.

“Don haka da wannan aikin ya zo na babban bankin duniya da gwamnatin tarayya da jiha muka ga yadace aikin Kasarawa da Bado da aka barshi shekara da shekarru ba a kammala ba tun kafin zuwanmu a kawo shi a fadada da inganta shi.” a cewar Tambuwal.

Ya yi kira ga mutanen yankin su tsaya su tsare kayansu kar su jira gwamnati wurin tsare aikin domin ya dore.

Da farko kwamishinan ruwa na jiha Umar Muhammad Bature a jawabinsa ya fadi yanda aikin yake zai rika samar da galan dubu 450 a kowane yini, an gina rijiyar murtsatse biyar da za ta rika amfani da hasken rana.

Hakama sun sanya bututun ruwa(pipe) a Bado da kewaye guda dubu 20,000, sun gyara wasu gine-gine a kusa da aikin.

A bayanin da Managarciya ta samu a yanzu kusan gidaje 200 suka ja ruwan a unguwar Bado dukan wadanda suka ja ruwan sun biya 5,500 rabin kudin da aka shardanta biya na jan ruwa 11,000.

A bayanin da ke kasa an ragewa duk wanda ya aminta ya ja ruwan zai biya rabin kafin wata mai kamawa, amma kudin wata-wata naira 1000 za a ci gaba da biya har yanda Allah ya so.

Jami’in da aka tattauna da shi ya bayyana al’umma sun yi farinciki da lamarin ganin wannan wata hanya ce mai inganci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *