Spread the love

 

Daga Aminu Dankaduna Amanawa, Sokoto.

Wani babban abin da yafi jan hankalin jama’ar Najeriya a wannan lokacin da ake ciki, bai wuce turka-turkar dake wakana ba tsakanin gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad Elrufa’i, da kungiyar kwadago wanda shugaban kungiyar kwadago na kasa NLC Comrade Ayuba Wabba ke jagorantar gudanar da zanga-zangar kin jinin matakin da gwamnan na Kaduna ya dauka na dakatar da ma’aikatan kananan hukumomi, da wasu tarin ma’aikatan jihar da sunan rage yawan kudaden da ma’aikatan ke lakumewa na dan abin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya.
Wannan kusan shi ne abin da bayanai, kafofin yada labarai dama wadanda lamarin ya shafa ke bayyanawa a matsayin dalilin dashi gwamnan ke bayyanawa daya sanya daukar matakin dakatar da ma’aikatan, a lokacin da dubban dalibai a jihar suka kammala karatu a manyan makarantun gaba da sakandiri daban daban dake ciki da wajen jihar ta Kaduna dake da burin samun aikin dogaro da kansu, domin tallafawa kansu da iyalan su.
Baya ga wannan ma, jihar ta Kaduna kusan na daga cikin jihohin da matsalar tsaro ke addaba kama da ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, rikicin kabilanci dana addini da sauran su, da galibi masu lura kan lamurran yau da kullum ke alakantawa da rashin ayukkan yi da jama’a ke fama dashi, a matsayin daya daga cikin manyan abubuwan dake zama tarnaki da dorewar zaman lafiyar, duk wata gwamnati data kasa shawo kan matsalar rashin ayukkan yi musamman ga matasa, koma koyar dasu sana’oin hannu, kamar yanda da yawa daga cikin masu lura kan lamurran na yau da kullum ke bayyana.
Koda yake ba wannan ne karon farko ba da gwamnan ke daukar irin matakin daya doka na korar ma’aikata, inda ko a baya sai bayanai suka Ambato gwamnan ya dakatar da malaman makarantun jihar da sunan samar da ingatattun da zasu ciyar da ilimin jihar ta Kaduna a gaba, ganin yanda bangaren ke da nakasu na iya cimma nasarar da aka tsara 100 bisa 100 na samar da ingataccen ilimi ga yaran jihar ta Kaduna.
Duk da yake a wani bangare za’a iya duba cikin tsanaki kan dalillan da suka sanya gwamnan daukar wannan matakin, amma a irin wannan hali da yanayin da ake ciki daukar irin wannan matakin sam bai kamata ba, domin galibin ma’aikatan aikin da suke gudanarwa kusan shine abinda suka dogara wajen ciyar da iyalan su, dama tallafawa abokan arziki su iya tafiyar da rayuwar cikin rufin assiri.
“Duk dan daya hana babarsa bacci tofa tabbas shima fa bazai runtsa ba, wannan kusan Karin magana ne da malam bahaushe kanyi amfani dashi wajen fitar da sakon dake zuciyar sa a fakaice, koda arashi da masu iya magana kance ya kamma bakauye, domin kuwa sanin ko wane gwamnan jihar ta Kaduna Malam Nasir Elrufa’i na daga cikin sahun gaba-gaba da a baya yasha shiga a sahun ‘yan kwadago domin gudanar da zanga-zanga kan lamurran da suka shafi kasa, musamman na tsaro a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa GoodLuck Jonathan.
Sai dai wanzam baka son jarfa, abin da yafi bawa mutane mamaki da shine irin kalaman gwamnan a kwana na biyu da aka shiga zanga-zangar, na neman shugaban kungiyar kwadago ta kasa N.L.C Comrade Ayuba Wabba, bisa zargin sa da yunkurin durkusar da tattalin arzikin jihar a zanga-zangar da suke da takai da dakatar da harkokin yau da kullum, na aiki, kasuwanci, sufuri dama hasken wutar lantarki, baya ga wannan ma, a wata sanarwa da ta ce, “gwamnati za ta kori dukkanin ma’aikatan jinya da ba su kai matakin aiki na 14 ba saboda yajin aikin da suka shiga ba bisa ka’ida ba, dama na barazanar korar duk wani ma’aikacin jami’ar jihar da ya kaurace wa aiki.
Dama na umarnin da gwamnati ta bayar ga dukkanin ma’aikatun jihar nasu gabatar da rijistar ma’aikatan da ke zuwa aiki ga sakataren gwamnati da kuma kwamishinan ilimi.
Lamarin dai kusan yaso ya koma almara ko wasan kalamai tsakanin gwamnatin da kungiyar kwadago, inda a bayanin kakakin kungiyar kwadagon na kasa Comrade Nasir Kabir, ya bayyana cewa ita kungiyar na neman gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ruwa a jallo, dama bada tukuici ga wanda ya ganshi zai kamashi.
Da akwai karin maganar da malam bahaushe kanyi na cewa, idan manyan giwaye na fada to tabbas kananan ciyayi ne ke shan wuya, domin kuwa musayar kalamai da ake tsakanin gwamnati da kungiyar ba mai shan wahala kamar masu karamin karfi watau talakawa, da basu da abin sakawa bakin salati face sai sun fita a rana sun nema, duk kuwa da yake cewa kungiyar na fafutika ne kan ma’aikata musamman ma na kananan hukumomi, bayan da ita kuma gwamnatin ta kafe kan cewa, duk abunda take tanayi ne domin samun kudaden inganta jihar ta Kaduna da ake yiwa kirari da garin gwamna.
Yanzu dai abin lura muhimmaci shine samun damar yin sasanci a tsakanin bangarorin biyu, kusan shine mafi a’ala ko baya ga janyewa yajin aikin, domin hangen gaba, kuma yanada muhimmancin gwamnatin kadunan dama ire-iren ta da su rika fitowa fili suna bayani ga talakawan su, kan duk wani shiri da suke son fitowa dashi ta yanda talakawa da sauran al’umma zasu fahimta kuma su amfana da shirin da gwamnati ke cewa tana yine domin amfanin su kasancewar ana mulkin dimokuradiiya ne, da talakawa keda damar yin zanga-zanga, muddin bata sabawa dokokin kasa ba, dama neman bayanin kan gwamnati na abunda ya shige masu duhu.
Yayin da a dayan bangaren kuwa, yana da matukar muhimmanci kungiyar kwadagon ta N.L.C ta zage damtse wajen tabbatar da gaskiya a tsakanin masu rike da madafun iko da talakawa, domin sune kadai hanyar da ta ragewa talakawa da zasu jagorancesu ga samun hakkokin su ga mahukunta.
A karshe ya kyautu talakawa su kara zage damtse wajen yin addu’a ta fatan alkhairi ga talakawa, a maimakon yin kalaman da basu dace ba, domin kuwa samun nasarar su itace nasarar talaka, akasin hakan kuwa talakawan ne dai zasu cigaba da dandana kudar su.
Aminu Dankaduna Amanawa,
Dan Jarida ne a Sokoto.
07065654787/09035522212
Amanawa.kd@gmail.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *