Spread the love

Gwamnan Delta Ifenyi Okowa a jiya Talata ya saukar da dukan mambobin majalisar zartawar jiha da suka haɗa da kwamishinoni da sakataren gwamnati da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da masu ba shi shawara na musamman.

A zantawa da manema labarai  kwamishinan yada labarai mai barin gado Mista Charles Aniagwu yana tare da rakitar sakataren yada labarai na gwamna Olisa ya ce  wasu matsayar an dauke ta ne a taron da aka gudanar  a gidan gwamnati dake Asaba, wani mataki ne na gyara fasalin gwamnati domin samun cigaba.

Ya ce gwamnan ya godewa ma tsoffin muƙarabban da gudunmuwar da suka bayar tsawon shekara shida.

Ya umarci duk wanda aka sauke ya mika ragamar ofis ga jami’i mafi mukami a ma’aikatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *