Spread the love

EFCC sun gayyaci shugabannin jam’iyar PDP domin karba wasu tambayoyi a zargin da ake yi masu na sama da fadi da zamba cikin aminci na ofis nasu a wasu kudi da aka wawure.

Wannan yana zuwa ne bayan wata guda da daya daga cikin jigon jam’iyar PDP Kazeem Afegbua ya aika korafinsa ga hukumar EFCC kan ta binciki jagorancin Uche Secondus domin sun yi sama da fadi da kudin jam’iya.

A takardar da ya aikawa EFCC a 17 ga watan Mayu 2021 ya nemi hukumar ta roki sanin wasu bayanai ga shugabannin jam’iyar  saboda akwai almundahana a ciki.

Hukumar ta gayyaci shugaba na kasa da Odita da Sakataren tsare-tsare da daraktan kudi su bayyana a 19 zuwa 21  ga watan mayun 2021.

EFCC ta nemi su karba gayyatar tare da takardun da suka kamata da suka kunshi fom da aka sayar tun tun Junairun 2017 zuwa yanzu.

Secodus ya karyata zargin har ya sanya karar mai zarginsu da biya shi biliyan daya kan bacin suna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *