Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Gwamnan jihar zamfara Bello Mohammed Matawalle, ya tabbatar wa ma’aikatan jihar cewa duk da irin tasirin da cutar COVID-19 tayi ga tattalin arzikin Duniya da ayyukan ‘yan ta’adda a jihar, gwamnatinsa ba za ta yarda tayi abun da zai kawo matsala ga jin dadin su ba.

Gwamnan ya bayar da wannan tabbacin ne yau a lokacin da yake gabatar da sakonsa na Sallah ga mutanen jihar ta zamfara, a fadar gwamnati da ke Gusau babban birnin jihar.

Yace, ya lura da cewa jihohi da yawa da suka sha wahala a dalilin wannan cutar sun yi kokarin rage yawan ma’aikatan su, kasan cewar basu da cikakken karfin daukar nauyin su, Matawalle ya ci gaba da cewa hakan ba za ta faru ba a karkashin jagorancin sa.

Ya kara da cewa maimakon rage su, gwamnatinsa na ci gaba da kirkirar hanyoyin biyan bukatun mutane ta hanyar sayen kayayyakin abinci da yawa, wadanda aka rarraba a dukkanin rumfunan zabe na jihar 2,516, dàke fadin jihar. Da samar da taimako na kayan abinci ga wuraren ibada cikin wannan watan na Azumi.

“Bayan bada taimako ga wuraren ibada mun kuma kara bada irin wannan taimakon ga majalisar sarakunan zamfara, da gidan gyara halin ka, da gidan marayu da kuma ma’aikatan gwamnati, mun sayi shadda da atamfa har guda 40,000 kuma an rarraba su ga marayu da sauran masu karamin karfi domin basu damar gudanar da bikin karamar sallah cikin farin ciki da walwala.

” Bayan haka mun tallafawa wadanda ke tsare a gidan yari da gudum mawar buhu huna 400 na abinci iri daban-daban ga fursunonin gidan dake a Gusau na gyara halin ka duk a cikin wannan watan na Ramalan”. inji matawalle.

Ya ce duk da barazanar da ‘yan ta’adda ke yi da kuma illolin da ke tattare da ta’addaan cin a wannan jihar, bazai kawo matsalar da zata sa gwamnatin sa bar yin ayyukkan more rayuwa ga jama’ar sa.

Daga nan sai ya yiwa mutanen jihar barka da Sallah tare da rokon su da su ci gaba da yin addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da ci gaba da kiyaye kyawawan dabi’u da darussan da aka koya a cikin wata mai Alfarma da albarka. Ya kara yin kira da a yawaita yin addu’o’in kawo karshen ta’addanci a jihar da kuma kasa baki daya.

Ya taya al’ummar musulmin jihar murnar ganin wata Ramalana da Sallah tare da godewa masu hannu da shuni da suka bayar da dukiyoyinsu ga marayu, zawarawa, da sauran kungiyoyin marasa karfi a cikin al’umma duk a cikin wannan wata mai alfarma, yana mai fatan za su ci gaba da wannan karam cin na jin kai koda wannan watan ya wuce.

Ya kuma yaba wa malaman addinin musulunci masu wa’azi da shugabannin al’umma kan wa’azin zaman lafiya a duk wannan wata mai alfarma, ya kuma yaba da ci gaba da goyon baya da addu’o’in da jama’ar jihar ke yi wa gwamnati, hakama ya kara yin kira ga iyaye da su tabbatar da cewa ’ya’yansu sun sanya tufafin da suka dace a ko yaushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *