Spread the love

Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyar PDP mai adawa a Nijeriya Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana jam’iyar APC mai mulki a matsayin wadda ba ta kasa ba ce  domin ba ruwanta da kare hakkin ‘yan kasa.

Tambuwal ya fadi hakan ne a Ibadan jihar Oyo a wurin bukin dare da aka shirya masu kafin gudanar da taron gwamnonin PDP da za su yi a jihar kan tsaro da tattalin arziki.

Tambuwal ya ce ba za su saduda ba domin sun tabbata makiyan kasar Nijeriya ‘yan Nijeriya za su yi aikin da za a samu  nasara kansu.

Ya ce sun dauki alkawalin PDP za ta rike Nijeriya a 2023 hakan ya sanya suke wannan zagayen jiha bayan jiha sun yi taro a Benue ga su Ibadan daga nan kuma za su tafi wata jiha daban kan kudirinsu na ceto Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *