Spread the love
 
 
 
Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ne ya yi wannan kiran a ranar Assabar lokacin da yake karɓar Sarkin musulmi da ya kawo masa gaisuwar barka da sallah ya nemi APC a jihar Sakkwato da su jingine duk wani abu da suke ji su zo a haɗa kai cikin gwamnatinsa don ciyar da jiha a gaba.
Gwamnan ya jinjinawa sarkin musulmi kan yunƙurin da ya yi na shiga cikin maganar yajin aiki ma’aikatan shari’a da majalisar dokokin jihohi don samar da maslaha.
 
Ya ce salon jagorancin Sarkin Musulmi wurin taimakawa gwamnati a ƙasa da jihohi don samar da daidaito da adalci abin yabawa ne.
Gwamna Tambuwal ya godewa sauran sarakuna da malamai a jiha kan haɗin kan da suke baiwa gwamnatinsa ya ce gwamnatin jiha ta soma gyaran wasu gidajen uwayen ƙasa a jiha da zimmar aikin zai  ƙarfafa su; su cigaba da aikin da suke yi na samar da zaman lafiya da tsaro.
 
 
Ya bayyana a halin yanzu an fara gyaran fadar uban kasa 21 kan haka ya ba da tabbacin bayan kammala wadanda aka fara da su za a sake zakulo wasu.
Don haka ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a jiha su cigaba da ba su goyon baya da shawarwarin da suke baiwa gwamnati tun shigowarta domin cigaban jiha.
 
Haka kuma Tambuwal ya yi kira ga ‘yan adawa a jihar su hade da shi domin kawo cigaba a jihar hakan yakamata a mayarwa hankali a jingine duk wani abu da ake ji a tsakanin juna a tun kari abin da ke gaba a manta da baya don kawai cigaban jihar ta Sakkwato.
Duk yunkurin jin tabakin shugaban riko na jam’iyar APC a Sakkwato Alhaji Isah Sadaik Acida abin ya ci tura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *