Spread the love

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya sanar da dandazon magoya bayansa da suka kai masa gaisuwar Sallah a Assabar data gaba buƙatar da yake da ita guda ɗaya da yake son Allah ya cika masa a duniyar nan.

Sanata Wamakko wanda yake tsohon gwamna ne a  jihar Sakkwato da ya shafe shekara takwas yana mulkin jihar ya jawo hankalin duk wani masoyinsa da ya sani ga buƙatar da yake da ita wurin Allah don haka duk wani mai sonsa ya rika yi masa addu’a burinsa ya cika.

Wamakko ya ba da tarihin ni’imomin da Allah ya yi masa tun sanda ya soma aikin gwamnati ana biyansa naira 50 har zuwa yanzu da ake ba shi miliyoyin kudi a matsayin albashi.

“Duk abin da Allah ke yi wa mutum na ni’ima ya yi gare ni don haka nake gode masa, a yanzu ban da wani buri na shugabanci kowane iri ne bukatar da nake da ita na gama lafiya da duniyar nan, Allah ina rokonka kasa na gama lafiya.” a cewar Wamakko.

Sanatan ya ce ba wani mulki a gabansa daga cikin wanda masoya ke roka masa ya samu, abin da ya sa a gaba shi ne gamawa lafiya ya cika da imani.

Ya godewa ɗimbin magoya bayansa da suka kawo masa gaisuwar Sallah da yi masu fatan alheri da komawa gidajensu lafiya da cigaba da zama lafiya a duk in da suke a rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *