Spread the love

Uwar gidan Gwamnan Sokoto Hajiya Mariya Aminu Waziri Tambuwal ta yi zaman cin abinci na musamman da yara marayu a babban gidan marayu da gwamnati ke kula da shi dake Gawon nama a cikin birnin jiha.

Cin abincin ya gudana ne karkashin kulawar Gidauniyarta waton Mariya Tambuwal Development Initiative da manufar faranta rayuwar yaran da kuma jawo su a jiki.

Bayan wasa da yara wasu daga cikinsu Mariya Tambuwal ta yi jawabinta ga al’umma ta ce akwai bukatar mawadata da muke da su rika kulawa da marayu, su nuna masu soyayya musamman marasa galihu a jiha domin taimakawa rayuwa.

Tambuwal ta yi alƙawalin cigaba da tallafawa marayun da nuna soyayyarta gare su, shirya wannan cin abinci wani ɓangare ne na ƙoƙarin da take yi na ƙarfafa walwalar marayu a jihar Sakkwato.

Wannan yana cikin halayyar uwar gidan Gwamna takan ziyarci marayun lokaci-lokaci kulawarta gare su ya sanya ake kiranta da uwar marayu.

An gudanar da addu’o’i na musamman domin samun nasarar marayun a rayuwa.

Jagororin mata a jihar suna cikin waɗanda suka raka Uwar gidan gwamna a gidan marayu mallakar jihar Sakkwato.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *