Spread the love

 

‘Yan sanda sun kubutar da wata yarinya da aka kulle a keji tsawon wata 8 a yanzu tana samun sauki tana dawowa cikin hayyacinta a asibiti.

Yarinyar mai suna Joy Emmanuel, mai shekara 12 ta bayyana cewa an rika hana ta abinci tsawon wannan lokaci tare da hadin bakin gwaggonta da mijinta.

Bayan tonuwar asirin ma’auratan, sun shaida wa ’yan sanda cewa yarinyar na fama da tabin hankali, amma da aka gudanar da bincike aka gano cewa karya suke yi.

Kakakin ’yan sandan jihar Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar, ya ce an ceto yarinyar tare da tsare wanda suka rufeta a caji ofis din da ke Dadin Kowa.

“Sun tsare yarinyar cikin wani keji da ke cikin gidansu na tsawon wata takwas ba tare da isashshen abinci ba.

“Bayan jami’anmu sun balle kejin, yarinyar ta kasa tafiya saboda tsananin yunwa da ya galabaitar da ita.

“Mun same ta cikin wani mummunan yanayi, inda a ciki kejin da aka kulle ta take bayan gida da fitsari.

“Amma daga baya mun dauke ta zuwa asibitin kwararru don duba lafiyarta,” a cewar kakakin ’yan sandan.

Kazalika, ya ce za a mika yarinyar da wadanda suka daure ta ga Hukumar Hana Fataucin Mutane da Dangoginsu ta Kasa (NAPTIP), don daukar matakin da ya kamata.

A halin da ake ciki kungiyoyin sa kai a jihar suna kai gudunmuwarsu na taimakon yarinyar a asibiti domin kara mata guiwa da yin tir da abin da aka aikata mata.

Wannan bakin hali da cuta ana samunsa a cikin al’umma a yanzu jefi-jefi a kwanan baya ma haka aka samu wani uba ya daure dansa a jihar Kebbi cikin dabbobi tsawon lokaci.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *