Spread the love
A duk shekara a bukin sallah  an al’adanci Mai martaba Sarkin Musulmi yakan kawo ziyarar barka da Sallah ga gwamna mai ci  a gidan gwamnatin jihar Sakkwato.
A wannan shekarar kamar koyaushe Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya kai gaisuwar sallah ga Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal a gidan saukar shugaban ƙasa dake birnin jiha.
Sarki ya kai gaisuwar  ne a kwana uku da sallah sai dai kwamishinonin Tambuwal bakwai ne kawai daga cikin sama da 20 suka halarci wurin.
Masu bayar da shawara  na musamman ga Gwamnan ba su kai biyar ba.
A dakin taron an ware kujera 22 domin zaman kwamishinonin amma ba su halarta ba, wannan kusan sabon abu ne ya faru Sarkin musulmi ya zo gaisuwar sallah ba a samu Kwamishina sama da 10 ba  domin tarbarsa kamar yadda uwayen ƙasa ke yin kara a duk shekara.
Lamarin ya ja hankalin Managarciya ne ganin yanda uwayen kasa suka halarta da yawa, wurin  da aka ware masu ya cika sosai saɓanin in da aka warewa muƙarraban gwamnatin jiha.
Sarkin musulmi a jawabinsa ya ce  akwai buƙatar a kawo ƙarshen yajin aikin ma’aikatan shari’a da Majalisar dokokin jihohi a wannan lokaci don haka zai zauna da ma’aikatan da zimmar samar maslaha kan lamarin.
Sa’ad ya yabawa Tambuwal kan cigaban da yake samarwa a jiha, ya nuna gamsuwarsa ga irin haɗin kai da ke tsakanin gwamnati da majalisar dokoki da ɓangaren shari’a ya nemi a daure da hakan domin samun cigaban jiha.
Mai baiwa gwamna shawara kan harkokin yaɗa labarai Muhammad Bello a lokacin da aka tambaye shi dalilin rashin zuwan kwamishinonin ya ce yana yiwu wani uzuri ne ya hana masu zuwa duk da an tanadar masu wurin zama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *