Spread the love
  1. Shugaban Majalisar Dattawa Ya Taya Al’ummar Musulmi Murnar Ranar Sallah
Daga M. A. Umar, Abuja
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya taya daukacin al’ummar musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan.
Lawan ya kuma yi ma al’ummar Musulmi fatan barka da ranar karamar sallah ta Eid-el Fitr.
Bayanin na kunshe ne a takardar manema labarai da mai baiwa shugaban shawara a kan aikin jarida, Mista Ola Awoniya ya sanyawa hannu.
Yace, “kowane musulmin kwarai yana murna da yin azumin watan Ramadan, wanda babban ginshiki ne a addinin musulunci. Allah madaukakin sarki ya bamu ladar wannan ibada,  ya kuma biya mana bukatan mu da na iyalanmu da kasar mu.
“Duba da halin rashin tsaro da kalubalen tattalin arziki da mu ke fuskanta, kasar mu Najeriya tana bukatar adduar ko wane mai kishin kasa a yanzu fiye da kowane lokaci domin samun zaman lafiya, hadin kai da cigaba kamar yadda shugabannin mu na baya suka dora turba.
“Ina tabbtar mana da cewa gwamnati, ciki har da majalisar dokoki ta tarayya, ba zata yi kasa a guiwa ba kan jajircewar ta na ganin an samar da ingantaccen tsaro a kasa da zai ba kowane dan kasa nagari ‘yancin zaman lafiya da yin harkokinsa a ko’ina ya zaba.
“Mu cigaba da jajircewa a fatan mu na kasar mu Najeriya ta zama abin farin ciki da alfahari ga dukkan yan kasar”.
Shugaban majalisar dattawa, yayi fatan cewa al’ummar musulmi zasu gudanar da bukukuwan sallah cikin jin dadi da zaman lafiya tare da iyalan su, abokan su da kuma masu karafin karfi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *