Gwamnatin tarayya tana iya ƙoƙarinta don kawo ƙarshen ta’addanci a Nijeriya—Malami

Ministan shari’a Abubakar Malami ya ce gwamnatin tarayya tana iya ƙoƙarinta don kawo ƙarshen ta’addanci a Nijeriya.
Ministan Shari’a a saƙonsa na barka da sallah ga al’ummar Nijeriya wanda mataimaki na musamman gare shi kan harkokin yaɗa labarai Dakta Umar Jibrilu Gwandu ya rabawa manema labarai ya ce bayan gurfana masu daukar nauyin ‘yan ta’addan Boko haram su 400 gwamnati na ɗaukar matakan daƙile aiyukkan ‘yan ta’adda a Nijeriya.
Ya ce nan ba da jimawa ba ma’aikatar shari’a za ta samar da kotu ta musamman don hukunta masu tayar da ƙayar bai.
Abubakar Malami ya taya musulman Nijeriya barka da sallar wannan shekara a kuma riƙe darussan da aka koya a cikin watan Ramadan.
Ministan ya jinjinawa malamai kan karantar da mutane da suka yi a watan Azumi wannan abin yabawa ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *