Spread the love

 

Gwamnatin jihar Sakkwato karkashin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta fitar sanarwa sake mayar da Sarkin Kabin Yabo Muhammad Maiturare na biyu  bayan da gwamnatin tsohon gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko ta sauya masa garin Sarauta a  lokacinta.
Tambuwal a takardar da sakataren gwamnatinsa Sa’idu Umar ya sanyawa hannu ya umarci kwamishinan shari’a ya tattauna da majalisar sarkin musulmi domin mayar da basaraken a  karamar hukumar Yabo domin cigaba da jagoranci a matsayin Sarkin Kabin Yabo.
Hakan ke nuna zai baro daga in da aka sauya masa wurin aiki a kasar Dandinmahe cikin karamar hukumar Shagari, bayan nazarin da aka yi a sauyin.
Uban kasar na Yabo Muhammadu Maiturare an yi mashi sauyi wurin aiki ne a lokacin Sanata Wamakko kan zarginsa da rashin biyayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *