Spread the love

 

 

 

Mahara dauke da muyagun makamai  sun kashe a ƙalla mutum 11 sun yi wa uku rauni a garin Tsatkiya ƙaramar hukumar Safana jihar Katsina a ranar Assabar kamar yadda manema labarai suka samu bayani.

Mutum ukun da suka samu rauni suna karɓar magani a Dutsin-Ma

Manema labarai sun hada bayanin an kawo harin ne a garin 9:30 na safe.

Ana hasashen ramuwar gayya ce suka zo yi kan kashe masu ɗaya daga cikin mutanen da ke masu kwarmato da mutanen gari suka yi.

Kwana hudu da suka  kawo harin bayan kashe mai kai masu kwarmato infoma.

Wata majiya ta shedawa daily trust Maharan sun zo saman babura suka riƙa harbi abin da ya kai da mutuwar mutum 11 mutanen ƙauyen sun cigaba da barin gidajensu suna komawa Dutsin-Ma gudun hijira.

Mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda ta Katsina SP Gambo Isa ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce mutum uku ne ba 11 ba kamar yadda mutanen garin suka ambata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *