Spread the love

Mutum takwas sun rasu wasu biyar sun samu raunukka a haɗarin mota da ya faru a kwana bakwai kan hanyar Minna zuwa Lambata a jihar Neja.

Haɗarin ya faru ne da daren Jumu’a da wata motar jigila ta Katsina.

Motar tana ɗauke da mata da maza ta taso daga Minna zuwa Katsina.

A bayanin da jami’in kiyaye haɗurra a Lambata Kwamanda Babatunde Onemols ya yi ya ce lamarin ya faru ne saboda fashewar tayar mota direban ya kasa riƙe mota.

Ya ce fasinjojin 13 ne lamarin ya ritsa da su bakwai suka mutu nan take ɗayan kuma ya rasu a cibiyar kiyon lafiya ta Gawu Babangida.

Sauran kuma suka samu raunuka a jikinsu har yanzu suna kan karɓar magani a asibiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *