Spread the love
A sallar bana ma Buhari zai yi ta a fadar shugaban ƙasa, ba za a kai masa yawon sallah ba.
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai bi sahun mutanen duniya wurin gudanar da bukin sallah ƙarama a ƙarshen watan Ramadan ya ba da unarnin a taƙaita shagullan saboda halin da duniya ke ciki.
Kan haka shugaban ƙasa da iyalansa da wasu muƙarabansa za su gudanar Sallar idinsu a fadar shugaban ƙasa tare da kiyaye sharuɗɗan dokokin Korona.
Haka kuma yawon sallah da ake yi na al’ada ga shugaban ƙasa a wannan shekarar ma an soke ziyarar ta ‘yan siyasa da jagororin al’umma.
Shugaba Buhari ya godewa malamai da sauran shugabannin addini kan yi wa ƙasa addu’a da suke yi domin samun cigaban ƙasa da mutanenta.
Ya yi kira ga jagorori su yi magana da matasansu kan hanƙoran da suke yi na ƙara zuba wutar rikici

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *