Spread the love
Sanata Wamakko ya soma rabon kayan Sallah ga mabuƙata a Sakkwato
Sanata Aliyu Magatakarda Wanakko ya kaddamar da rabon kayan sallah ga mabukata maza da mata a Sakkwato.
Sanatan wanda yake tsohon gwamnan Sakkwato ne ya  soma rabon Turamen Atamfa da kudi inda aka Fara da Mata Matasa, tsoffi da Kuma masu lalurar jiki.
A kalla Mata sama da Dubu uku ne ake saran su ci gajiyar wannan tallafin. Kamar yadda jami’i ga Wamakkon ya sanar.
Ya ce  tsarin a  Lahadi za a ci gaba da rabon kayan ga Maza Matasa, da Dattijai da Kuma masu lalurar jiki.
“Idan dai za a iya tunawa a Shekarar bara da ta gabata, ba a Sami damar gabatar da irin hakan ba saboda dalilai na murar mashako wato COVID 19, duk da dai an yi rabon kayan a bangare – bangare.” a cewarsa.
Sanatan yana wannan hoɓɓasar tun yana gwamna har zuwa yanzu bai nuna gazawarsa ba ga taimakon al’umma.
Managarciya ta fahimci a jihar Sakkwato da za a sami ‘yan siyasar da za su koyi da shi da za a samu ragewar talauci ƙwarai da gaske.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *