Spread the love

Gwamnatin jihar Sakkwato karkashin jagorancin Aminu Waziri Tambuwal ta ce za ta samar da makiyaya ta zamani a hadakar da za ta yi da kasar Indunisiya da bankin musulunci da kuma bankin bayar da rance ga manoma a Nijeriya(NIRSAL), a kokarinta na kawar da aiyukkan ‘yan ta’adda za a samar da cibiyoyin kiyon lafiyar dabbobi  na zamani a dukkan jihar.

Gwamna Tambuwal ya sanar da hakan ne a lokacin da yake karbar bakuncin jekadan kasar Indunisiya a Nijeriya AVM Usra Hendra Harahap da tawagarsa domin ziyarar aiki a Sakkwato.

Ya ce samar da wadanan cibiyoyin zai magance rikicin manoma da makiyaya abin da zai kara rage matsalar tsaro a kasar nan.

Tambuwal ya ce domin cimma burin hadakar ce mafita, wadda manoma a jihar za su amfana har da makwabta kuma dama ce ga makiyaya su yi lamurransu ba tsangwama.

Ya kara bayyana yadda gwamnatinsa ke baiwa noma muhimmanci da shirin da ake da shi na baiwa masana’antu masu zaman kansu dama domin samar da kamfunnan a jihar.

Bayan godiya da gudunmuwar da suke samu ga kasar Tambuwal ya zayyano fannin ilmi da daukar nauyin karatun ‘yan asalin jiha da harkar kiyon lafiya da aikin Gona duka suna bukatar Indunisiya ta sanya hannu a cikinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *