Spread the love

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aminta da dakatar da shugabar tashoshin jiragen ruwa(NPA) Hajiya Hadiza Bala Usman tare da kafa kwamitin bincikarta.

Dakatar da shugabar ya zo da bazata ganin yanda take cikin ‘yan gaban goshin gwamnatin tarayya  tun farko, musamman yanda alakarta da Gwamnan Kaduna take abin wasu ke hasashen shi ne ya samo mata mukamin da aka saukar da ita.

Haka wasu sun zargi siyasar 2023 ce cinye kujerar Usman ba wai tsamin dangantakar da ke tsakaninta da ministan sufuri Rotimi Amaechi ba.

An nada Hadiza 2016 biyo bayan cire Habib Abdullahi da aka yi wanda aka katse wa’adinsa na biyu da Buharin ya aiwatar.

An kafa kwamitin bincike da za su binciki yanda ta rika tafiyar da aikin nata tun da aka nadata domin fito gaskiyar zarge-zargen da ake yi mata.

Da wahalar gaske ta koma saman kujerarta domin a kasar Nijeriya da wuya a dakatar da mutum ya sake dawowa saman kujerar, a yanzu dai an baiwa wani dan jihar Kebbi Mukaddashin shugaba kafin kammala bincike ko ayyana wanda zai gade ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *