Spread the love

 

Wasu mahara sun yi garkuwa da Mai jego  ’yar jarida Amra Ahmad Diska, Edita a Hukumar Yada Lababarai ta Jihar Adamawa (ABC)  in da suka bar  jariririnta mai wata shidda da haihuwa.

“Da alamar ’yan bindigar sun je ne da nufin yin garkuwa da mijin ’yar jaridar amma da ba ba su same shi ba, sai suka tafi da mai jegon‚” inji wani shaidun gani da ido, wanda ya ce lamarin ya faru ne kafin wayewar garin Talata.

Mai Magana da yawun hukumar ‘yan sandan Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje ya ce an yi garkuwa da ’yar jaridar ce da misalin karfe 1 na dare a gidanta da ke  unguwar Mamba a wajen garin Yola.

DSP Nguroje ya ce tuni aka tura jami’ai su bi sawun masu garkuwar, kuma yana da kwarin gwiwar cewa za a kama su, su fuskanci hukunci kamar yadda dokar kasa ta tanadar.

Har kawo yau ‘yan bindigar ba  su tuntubi iyalan matar ba, kamar yadda suka sanar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *