Spread the love

Hukumar zabe za ta kirkiri sabbin rumfunan zabe 956 a Sakkwato

Hukumar zabe ta tsara kirkiro wasu sabbin rumfunan zabe 956 a Sakkwato.
Babban kwamishinan zabe Festus Okoye ya fitar da wannan bayanin a lokacin da yake tattaunawa da masu ruwa da tsaki a ranar Talata a Sakkwato.
Okoye ya ce aikin zai kara yawan rumfunan zabe daga 3,035 zuwa 3,991 tare da yawan masu jefa kuri’a 1,903 da 166.
Ya ce fadada rumfunan zaben da ake yi zai kara kawo sauki a wurin jefa kuri’a a Nijeriya, haka kuma akwai bukatar rage cikonson da ake da shi a rumfunan zaben.
A cewarsa a koyaushe jami’ansu na shan wahala a wurin daidaita masu zabe a natsake wanda hakan zai taimaka masu matuka.
Ya ce rage cinkoso a lokacin zabe abu ne da zai karawa zabe armashi da sahihanci abin da suka a gaba kenan, za su fito da tsarin fasahar zamani shi ma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *