Spread the love

 

Shugaban kasa Muhammadu  Buhari ya ba da umarnin rage albashin ma’aikatan wasu hukumomi da ma’aikatun Gwamnatin Tarayya.

Ministar Kudi, Zainab Ahmad ce ta sanar da hakan  ta ce umarnin na Buhari zai rage yawan kudaden da ake kashewa wajen gudanar da gwamnati.

“Shugaban Kasa ya umarci kwamitin tsara albashi, wanda nake jagoranta, tare da shugabar ma’aikatan tarayya da sauran ’yan kwamitin, cewa mu sake nazarin albashin ma’aikatun domin rage kudaden,’’ inji ta.

Ta bayyana hakan ne a jawabinta a  taron da aka yi kan rage kashe kudaden gudanar da gwamnati wanda hukumar yaki da almundahana (ICPC) ta shirya a Abuja ranar Talata.

Minsitar ta ce Gwamnatin za ta soke wasu kudade marasa ma’ana da ke kunshe a cikin kasafin shekara a ma’aikatun gwamnati.

Yawancin hukumomin gwamnati kan sanya kudaden sayen motocin aiki da kwamfutoci da sauransu a kasafinsu na kusan duk shekara.

Ministar ta ce, “Kasafin kudin kasar nan cike yake da tanadin kudaden ayyukan wanda  maimaitawa ne kawai kuma hakan bai dace ba.”

Da yake bayani a wurin taron, Shugaban ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye, ya ce matsalar ma’aikatan bogi a ma’aikatu na daga cikin matsalolin da ke sa albashin wuce misali.

A cewarsa, muddin aka kakkabe ma’aikatan bogi, to za a samu saukin abin da ake kashewa wurin biyan albashi.

A kwananan maganar rage albashin ma’aikata ake yi a Nijeriya in da aka mayar da hankali kansu da nuna kusan su kadai ne ke cinye arzikin kasa domin haka a rage albashinsu don abubuwa su daidaita, amma an manta yanda manya mutane masu rike da mukamai na siyasake karbar kudi da sauran bukatu na yau da kullum.

Rage albashin shugabannin siysa shi ne abin da yafi da cewa gwamnati ta duba domin za ka samu wani mai mukamin siyasa na karba abin da ma’aikaci 10 ba su karba ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *