Spread the love

 

Tsohon gwamnan jihar zamfara Alhaji Abdul’Aziz Yari Abubakar, ya kaddamar da tallafin kayan abinci da tufafi na fiye dà naira miliyan dari da biyar (105M) ga marayu dake a masarautu 17 dake jihar ta Zamfara.

Da yake jawabi jim kadan kafin kaddamar da rabon tallafin tsohon gwamnan ya baiwa marayun jihar ta Zamfara hakuri kasan cewar shi bai san da cewa gwamnati mai ci yanzu ta kasa tallafa masu ba.

Yari wanda ya maganta ta bakin Alhaji Abdullahi Maharazu Mafara, tsohon kwamishan lamurran addini yace, hakika idan Allah ya gwada muna badi warhaka kuma aka kara samun irin wannan akasin to da yardar Allah zasu dauki nauyin kusan duk marayen da ke Zamfara.

Yaja kunnen yan kwamitin da aka ba alhakin rabon kayan da su da ji tsoron Allah wajen gudanar da aikin da aka ba su domin ganin cewa kowa ya samu nashi kayan tallafin.

Ana shi jawabi, sakataren kwamitin tantance marayun dake masarautu 17, Alhaji Sanusi Liman Dan Alhaji yace, sun tantance marayu dubu biyar 5000, kuma kafin su bada sunayen marayun da zasu samu wannan tallafin saida suka bi cancanta. Inda ya kara da cewa sunyi la’ akari da yaran da aka kashe uwayen su sanadiyar harin yan bindiga, da kuma kone dukiyoyin su.

Sakataren ya ba da jadawalin rabon tallafin kamar haka, ko wace masarauta an zakulo marayu 277, maza 166, mata 101, amma mazabar Gusau zata samu kaso mafi tsoka, inda mata 332, da maza 222 zasu amfana.

Hakama sakataren kwamitin ya bayyana cewa, kowane maraya zai amfana da mudu shidda na gero, shidda na masara, biyu da rabi na shinkafa, biyu da rabi na sugar, shadda yadi biyar ga namiji da kuma turmin Atamfa daya.

Alhaji Sanusi Liman ya bayyana cewa bisa ga kiyasin da aka yi ko wane maraya zaya amfana da tallafin kayan abinci da tufafi da kuma kudin dunki da suka kama a kan kudi naira 21,000.

Bukin raba kayan wanda aka gudanar a Gusau babban birnin jihar zamfara ya samu halartar yayan jam’iyyar APC da ciki da wajen jihar.

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *