Malam Mahdi Umar Aliyu na cikin dattawan kungoyoyin masu lalura ta musamman a Sakkwato ya nemi gwamnatin jihar da ta waiwaye su da tallafi domin rage radadin wahalar da wasunsu ke ciki a wannan watan na Ramadan.

Malam Umar wanda ya taba neman zama shugaban karamar hukumar Sakkwato ta kudu shi ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai ya ce duk kokarin da gwamnatin Tambuwal ke yi a wurin kashe makudan kudi ga ciyar da mutane a watan Ramadan abin damuwa ne a ce mutane masu lalura ta musamman ba su amfana da abin da aka warewa talakawa da marasa karfi da masu lalura ta musamman ba.
Kungiyoyin sun daura wannan cikas nada nasaba da rashin jituwar kwamishiniyar ma’aikatar walwalar jama’a da mai baiwa gwamna shawara kan masu lalura ta musamman.
Kan haka yake kira gwamnatin jiha ta shigo ciki ta agaza masu a basu kudin tallafinsu na wata-wata da kuma nasu kaso na ciyarwa azumi a sauran kwankin da suka rage.
Malam Mahadi ya jinjinawa Tambuwal a kulawarsa da walwalar masu lalura ta musamman da fatan hakan zai dore.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *