Ibrahim Kabiru matashi ne dan shekara 19 dake sana’ar yankan farce a garin Benin na jihar Edo a kullum yakan samu cinikin 1,500, in ka hada su gaba daya yana samun N45,000.

Ibrahim, a cikin wata tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ce sana’ar na taimaka masa matuka wajen biyan bukatunsa na yau da kullum.

Ya ce ya yi kaura ne takanas tun daga jihar Sakkwato zuwa jihar ta Edo domin yin da sana’ar ya ce  duk da yake yana shan wahala matuka wajen yawo a cikin birnin yana neman kwastomomi, amma abin da yake samu yana isarshi.

 

Ibrahim ya shaida wa NAN cewa a baya yana sana’ar noman masara ne amma karancin jari ya sa tilas ya nemi wata sana’ar.

Ya ce ya kan karbi N100 a kan kowanne yankan farce da kankara, yayin da idan yanka ne zalla ba kankara ya kan karbi N50.

Mai yankan farcen ya ce jarin da ake bukata domin fara sana’ar bai wuce N1,000 ba domin sayen almakasai, soso, ruwa da kuma sabulu.

Da aka tambaye shi ko yana da niyyar komawa harkar noman idan ya samu jari sai ya ce eh, in da ya ce noma a yanzu dole yana bukatar jari.

Ya ce kasancewar bai yi karatun boko ba, sana’ar yankan farcen kawai zai yi  Benin  yi sai kuma ta noma a garinsu.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *