Spread the love

Kakakin majalisar dokokin jihar Sakkwato Alhaji Aminu Muhammad Achida a jawabinsa wurin rabon kayan azumi da kungiyar Buhari for All ta raba wa mabukata a Sakkwato ya ce mun wuce tsarin in mutum daya ya yanke hukunci ko dadi ko ba dadi sai kowa yabi shikenan

Aminu Achida ya ce “Siyasa ba gaba ba ce ba tashin hankali ba ne yakamata a yi ta zamani da wayewa da cigaba, ba wai a zauna a siyasar mutum guda kawai ba, lalura ce ta al’umma a bude lamarin ga al’umma, ba a ce in mutum daya ya yi hukunci ko dadi ko ba dadi dole kowa ya shiga.” a cewarsa.

Ya cigaba da cewa “Zamani ya zo mun wuce wannan tsari, don haka muka kawo tsari wanda kowa zai shigo a yi da shi hakan ya sa muke tare da gwamnatin jiha duk da mu mana a jam’iyarmu ta APC, harkar aiki ta hada mu da gwamna domin cigaban Sakkwato, hadin kanmu da gwamnati yana nan har karshen wannan lalurar.” in ji Kakakin Majalisa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *