Spread the love

‘Yan sanda a jihar Katsina sun kama wani barawo mai suna Ibrahim Lawal dan shekara 23 kan zarginsa da sace wayar hannu salula 273 da kudin zai kai kimanin miliyan 15.

Mai magana da yawun hukumar a jiha SP Gambo a lokacin da yake gabatar da wanda ake zargin da aka cabke a garin Daura ya ce sun kama wanda ake zargin a lokacin da ya shiga gidan wani Kamilu Ibrahim mai shekara 33 a unguwar rukunin gidaje na Shagari ya balle motarsa kirar BMW rukuni 3 ya sace waya da yawansu yakai 273 kudinsu zai kai miliyan 15.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *