Spread the love

Gwamantin Kaduna ta ce mutum 323 ne aka kashe yayin da 949 aka yi garkuwa da su a fadin jihar Kaduna daga Junairu zuwa Maris a 2021.

Kwamishinan cikin gida da tsaro a jihar Kaduna  Samuel Aruwan ne ya sanar da hakan a lokacin da yake bayar da bayanin zangon farko na shekara a taron tsaro da ya gudana a Kaduna.

A cewarsa maharan 64 aka kashe bangaren Kaduna ta tsakiya shi ne hare-haren yafi shafuwa bisa ga sauran yankunan.

Ya ce a cikin wadanda aka kashe mata 20 ne a cikinsu, 11 kanan yara, dukan mutum 236 sun rasa ransu ne a Birnin Gwari, Chikun, Igabi, Giwa da Kajuru.

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa’i ya koka kan yadda matsalar tsaro ta ta’azara a jihar da kasa baki daya, ya ba da tabbacin gwamnati za ta shawo kan matsalolin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *