Spread the love
Daga M. A. Umar, Abuja
 Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan tare da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni sun zo Kano don yi ma Sarki Aminu Ado Bayero ta’aziyyar mahaifiyarsa, Hajiya Maryam Ado
Hajiya Maryam Ado Bayero, wadda har ilayau ita ce mahaifiyar Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero ta rasu ne a ranar Asabar.
Haka nan kuma sun ziyarci Sokoto domin yi ma magajin garin Sokoto, Alhaji Hassan Danbaba ta’aziyar mahaifiyarsa, Hajiya Aishatu Ahmadu Bello.
Hajiya Aishatu, wadda ta rasu ranar Juma’a, diya ce ga marigayi firimiyan jihar arewa, Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto.
Bayanin hakan na kunshe ne a wata takardar manema labarai da Ola Awoniyi mai taimakawa shugaban majalisar bangaren labarai ya sanyawa hannu a yau.
Wadanda suka yi ma shugaban majalisar rakiya sun hada da shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Yahaya Abdullahi, Sanata Danjuma Goje, Sanata Ibrahim Gobir, Sanata Sahabi Ya’u da kuma Sanata Abdullahi Gumel.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *