Spread the love
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya taya ma’aikatan Najeriya murnar zagayowar ranar tunawa da ‘yan kwadago ta duniya.
Lawan yayi nuni da muhimmancin ranar 1 ga watan Mayu da aka ware a kowace shekara don jinjina ma yan kwadago a matsayin su na masu samar da wadata, da kuma duba yadda yadda za’a inganta wuraren ayyukan su da jin dadin su.
Yace, “ina mai taya ma’aikatan Najeriya murnar zagayowar wannan rana ta ma’aikata ta hadin kansu a duk duniya.
Shugaban majalisar ya bayyana hakan ne a wata takardar manema labarai, da mai taimaka wa shugaban majalisar akan aikin jarida Mista Ola Awoniyi ya fitar ya rabawa manema labarai a Abuja karshen makon nan.
Yace “Kungiyar kwadago ta Najeriya tana da tarihi abin alfahari tun kafata, tun daga kasaitacciyar gudumuwar da shuwagabannin da suka kafa ta, kamar su  Pa Micheal Imodu da mukarabban sa suka bada wajen gwagwarmayar neman yancin kan Najeriya, da kwato hakkin ma’aikata da sauran talakawa.
“A tsawon zamani, ma’aikatan Najeriya sun kasance a gaba wajen tafiyar da tattalin arziki, gina kasa da mukin dimokaradiyya a kasar nan.
“Ina mai yaba ma hakurin su, fahimtar su da jajircewar su a wannan kalubalen da kasar nan ke fuskanta.
“Majalisar dokoki ta tarayya ta yi imani da kyakykyawa rayuwa da jin dadin ma’aikata, kuma a koda yaushe za ta samar da goyon baya ga kowane yunkuri na magance kalubalen da suke fuskanta da kuma inganta wuraren ayyukan su.
“Ina tabbatar maku da alwashin majalisar dattawa ta tara wanda ya zo daidai da taken ta na “Aiki Don Najeriya.”
“Da wannan, zamu cigaba da goyon bayan ma’aikatan Najeriya ta wajen soke dokokin da su kai karo da hakkin yan kwadago, da assasa dokokin da za su mai da kasar mu kyakykyawan wuri ga ma’aikata.
Sai dai shugaban majalisar ya bukaci kungiyar kwadago da a ko yaushe ta rika fifita kasar nan a dukkan matsayin ta akan manufofi da tsare-tsare na gwamnati.
Lawan yayi fatan alheri ga yan kwadagon da fatan zasu yi bikin wannan rana cikin kwanciyar hankali.
Daga M. A. Umar, Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *