Spread the love

Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya kauracewa janazar diyar Sardauna Sakkwato Aisha Ahmadu Bello  wadda aka gudanar a masallacin Sarkin musulmi Muhammadu Bello a yau Alhamis bayan ta rasu a Dubai in da tayi jinyar rashin lafiyarta.

Mutane sun cika da mamakin rashin ganin sarkin musulmi a wurin janazar ganin tun sanda aka bayar da labarin rasuwarta a ranar Jumu’a data gabata yana cikin jihar Sakkwato kamin zuwan gawarta sai labari yake yawo yabar garin domin wasu dalilai da ba a bayyana ba.

Gawar Aisha Ahmadu Bello an binneta a makabarta Magajin Garin Sakkwato a unguwar Binanchi kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Margayiyar ta rasu a sanadiyar ciwon hawan jini mahaifiya ce ga magajin garin Sakkwato Alhaji Hassan Ahmad Danbaba shugaban hukumar raya gulaben Rima.

Sallar janazar ta samu halartar dimbin jama’a da suka hada da shugaban majalisar dattijai Ahmad Lawan da jagoran majalisa Yahaya Abdullahi da Sanata Aliyu Wamakko da Danjuma Goje da Ibrahim Gobir.

Sauran sun hada da Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da Yobe Mai Mala Buni da Kano Abdullahi Ganduje da tsohon gwaman Zamfara Abdul’aziz Yari da Aliko Dangote da Dahiru Mangal da Janar Aliyu Gusau da sauransu.

Wasu na zargin rashin halartar sarkin musulmi nada nasaba da rashin jituwar dake tsakaninsa da magajin garin ne duk da ba a tabbatar da hakan ba.

A lokuttan baya an samu tsamin dangantaka a tsakaninsu wadda manya a ƙasar nan suka daidaita tsakaninsu, amma duk da hakan an daina ganin fuskar Magajin Gari a fadar Sarkin musulmi.

Jami’in hulda da jama’a na majalisar sarkin musulmi Aminu Haliru Gidadawa ya ce shi bai da abin da zai ce game da zancen don ba shi yakamata a tuntuba da maganar ba.

Duk yunƙurin jin ta bakin Magajin Gari kan rashin halartar Sarkin Musulmi, ko yana da masaniya kan uzurin da ya hana halartar, sai dai  ba a samu nasarar hakan ba.

 Margayiyar ta rasu tana da shekara 76 ta bar ‘ya’ya 5 da jikoki 26.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *