Kamfanin Man fetur na kasa NNPC ya bayyana cewa ba za a samu kasonsa  a watan Mayu cikin  asusun kasa da ake rabawa jihohi, sun sanar da hakan ne a takardar da suka aikawa babban akawun gwamnatin tarayya a ranar Talatar data gabata.

A takardar da  shugaban kamfanin Mele Kyari ya ce biliyan 111.96 suka bayar na watan Afirilu amma a watan Mayu ba za su kawo ko sisi ba domin tabbatar da makamashi ya cigaba da zuwa cikin kasar ba tare da ya yanke ba.

A takardar ya fadawa babban akawun cewa litar Man fetur a watan Maris tana kamawa 184 ne a kowace lita sabanin yanda take a baya 128 wanda hakan ne ya taba tattalin arzikinsu wurin ware dimbin dukiya wajen biyan tallafin man fetur.

Rashin samun kudin Man fetur a asusun rabawa jihohi zai iya samar da gibi a kudin da za a ba jihohi  a watanni masu zuwa wanda zai sa su kasa biyan albashi a wasu jihohin.

Wata majiyar ta ce za a iya samun gibin biliyan 200 bambanci da sauran watanni da suka wuce.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *