Gidauniyar Sa’ar Mata ta raba abinci ga mabukata sama da 1000 a jihar Sakkwato.

Haka ma ta raba takardun jarabawar share fagen shiga jami’a waton JAMB   ga masu son shiga jami’a a kakar karatun 2021/2022.

Shugabar Gidauniyar Barista Sa’adatu Yanusa Muhammad ce ta jagorancin rabon kayan da aka  kaddamar a karamar hukumar Dange Shuni ta ce  wadanda za su amfana a kananan hukumomin Bodinga da Dange Shuni da Tureta ne dukansu a jihar Sakkwato, bayar da tallafin da zimmar  saukaka masu yanayin da ake ciki musamman a wannan watan na Ramadan, ta ce an samar da Gidauniyyar Sa’ar mata ne domin kula da aiyukkan taimakon al’umma musamman a yankin da ta fito.

Barista Sa’adatu ta ce a wannan lokacin da ake ibadar azumi mutane na bukatar tallafi musamman na abinci, ga wanda yake da hali bai kamata ya bari wannan watan ya wuce bai tallafawa mabukaci ko daya ne ba, hakan ya sa gidauniyar take son kar wannan alherin ya wuce ba ta yi iya nata kokari ba.

“Kamar yadda kuke gani  za mu raba tallafin abinci dana  karatu duk da ba mai yawa ba ne Allah ya sanya alheri cikinsa.” a cewarta

Ta ce tallafin  yakunshi kowane mataki na al’umma mabukata in da aka tantance wadanda za a baiwa a gaban mutane da wadanda za mu aika masu a gidajensu domin aiki ne na Allah kuma shi muke nufi da shi.

“Bayan shinkafa mun zakulo matasa 50 kamar yadda muka yi a shekarar data gabata za mu ba su fom na jarabawar share fagen shiga jami’a(JAMB) kamar na bayan su ma bayan sun shiga jam’iar za mu rika tallafa masu gwargwadon hali har su kammala karatunsu, ban da abin da yake gabana sama da in tsaya in tabbatar da yaraanmu sun samu ilmin da za su iya dogaro da kansu” a cewar Gimbiyar Dange.

Ta ce bayan wannan gidauniya  ta raba butoci da tabarmi a masallatanmu domin kara sauukaka ibada a wannan lokaci.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *