Spread the love
Tsohon shugaban ƙasar Nijeriya Olusegun Obansanjo ya aza harsashen gina gadar sama guda biyu da za a yi a kan titin Abdullahi Fodiyo a unguwar Runjin Sambo da kan titin Sarkin Musulmi Abubakar a unguwar Rijiyar Dorawa dake jihar Sakkwato.
Wannan aikin da yake matakin farawa majalisar zartarwar jiha wadda gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ke jagoranta ta aminta da a gudanar da aikin wata 10 da suka wuce.
Gwamnatin Tambuwal ta bayar da aikin ne ga kamfanin CCECC kan kuɗi biliyan 3.4, za a kammala aikin ne bayan watanni 22.
Obasanjo ya nuna gamsuwarsa da aikin za a yi mai nagarta ne musamman yanda gwamnati ta zaƙulo kamfanin da aka yarda da ƙwarewarsa a waɗan nan aiyukkan.
Ya yaba hangen nesar Gwamna ga samar da irin waɗan nan aiyukka da za su kawo cigaba a jiha da ƙara bunƙasa harkar sufuri.
A jawabin Tambuwal ya ce bunƙasa harkar sufuri abu ne dake ƙara inganta rayuwar al’umma bai kamata ka bar ta a baya ba, samar da gadar sama a Runjin Sambo tana cikin aiyukkan da yakamata a samar tun kafin yanzu.
Ya ce tana cikin aiyukkan da ba za a manta da su ba da za su cigaba da amfanar mutane wanda hakan mizani ne na cigaban jiha.
Gwamna Tambuwal ya ƙara da cewar a ƙarƙashin ma’aikatar filaye da gidaje ne aka bayar da waɗannan muhimman aiyukka biyar da suka haɗa da: Gadar sama a unguwar Runjin Sambo da Unguwar Rijiyar Dorawa da tagwayen hanyoyi a kan titin Waziri Abbas da Maituta da Gangaren tashar Illela zuwa hanya mai ɗaukewa zuwa garin  Achida.
Ya ce kwangilolin guda huɗu an baiwa kamfanin K&E da Solid Stone da Afdin da CCECC jimilar kuɗin da za a kashe wa aiyukkan gaba ɗaya biliya 10 da miliyan 943 da dubu 643 da 953.
Tambuwal ya bayyana wasu aiyukkan da ma’aikatar za ta kula da su bayan zaman  majalisar zartarwa, gina rukunan gidajen 342 da samar da hayar wajen gari daga kudu ga birnin jiha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *