Spread the love

Kwamiti mai ba majalisar Sarkin musulmi shawara kan lamurran addini ya yi taro da malamai da limaman jumu’a kan sha’anin Itikafi a watan Ramadan domin samun wata matsaya da za a iya dauka ga sha’anin ibadar, ganin yanda kalubalen zamani ya dabaibayi al’amurran.

Sarkin Malaman Sakkwato Malam Yahaya Boyi ne ya jagoranci zaman da aka yi a makarantar tunawa da Sarkin musulmi Maccido ya ce makasudin wanan taron domin sarkin musulmi ya aminta a kira dukan malamai a yi bayani game da Itikafi domin samar da tsari ga kalubalen zamani.

Ya ce ibadar itikafi sunnah ce da tabbata a dukkan littafan musulunci kan haka musulmai nada damar yinsa amma a bisa tsari.

Malam Mustafa Sidi Attahiru anasa gudunmuwa game da kalubalen zamani ya fadi yanda suka rika kama barayin babur da wayar hannu da suke yin shigar burtu a lokacin itikafi.

Haka ma ya fadi yanda suke shan wahalar masu itikafin a gefen tsafta da tarbiya wadda abin bukata ne masallatai su dauki matakin daidaita lamurra.

Malam Usman Jatau ya yi kira ga masallatai su samar da tsari na mutum ya tsaya a kusa da shi ba sai ya tafi nesa  domin gudanar da ibadar, a wannan halin ba bukatar sai mai son itikafi ya tafi wani masallaci nesa da gidansa.

A karshe bayan gudunmuwar malaman Malam Muhammad Lawal Maidoki ya godewa malamai da ba su tabbacin   za a kai shawarwarin da suka bayar gaban sarkin musulmi domin duba abin da za a yi kan lamarin.

Ya ce wannan taron shi ne irinsa na farko da aka yi a jihar kuma za a cigaba da yinsa lokaci-lokaci kan wasu ibadu tare da kiyaye lokacin taron gudun kar a sake kure lokaci kamar wannan.

“Mu sani kamar mu mayar da kanmu wasu gidadawa a kan lamurran duniya in sun shafi addininmu, a zauna tare da masana a samu maslaha shi ne yakamata” a cewarsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *