Spread the love

Mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto  Manir Muhammad Dan’iya ya wakilci   Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a  Jagorantar Zaman Majalisar Zartawa  wadda ta yi zamanta a dakin taro na fadar Gwamnatin Jiha.

 

Majalisar ta aminta da aiwatar da aiyukka da kudinsu yakai biliyan 11 aiyukkan sun hada da sake gina hanyar da ta tashi daga Shagari zuwa Tureta da sayo takin zamani na shekarar 2021, za su lakume kudi biliyan 7.6 da kuma biliyan 3.4 kowanensu.

Majalisar ta amince da ba da aiki kai tsaye a jiha ga duk wanda ya kammala karatun digiri da Babbar difiloma da sakamako mai darajja ta daya data biyu.

Kwamishinan yada labarai na jiha Isa Bajini Galadanci ne ya sanar da hakan bayan kammala zaman ya ce an ware wasu miliyan 115 domin sayen kayan duba bayani yanayi na jiha da gina dakin taro da zai iya daukar mutum 500 lokaci daya  a makarantar fasaha da kimiya  da kere-kere ta Umaru Ali Shinkafi kan kudi sama da miliyan 630, za a kammala ginin ne cikin wata 9.

Jagorantar majalisar wannan shi ne karo na farko da mataimakin gwamnan ya yi tun san da suka fara mulkin jiha ana kallon wannan damar da aka ba shi bai rasa nasaba da yanda ake ta yaɗa jitajitar cewa gwamna Tambuwal ba zai ba shi damar ya gade shi bayan kammala wa’adinsu ba.

Managarciya na hasashen  ba shi ragamar nada nasaba da zubawa wutar jita-jitar ruwa domin har yanzu lokacin harkokin siyasa bai soma ba, hakan zai sa Tambuwal ba zai so mutanen gwamnati su fara mayar da hankali ga magajinsa ba.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *