Spread the love
Allah ya yi wa ‘yar Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato rasuwa, Aishatu Ahmadu Bello.
Aishatu  ‘ya ce ta biyu ga marigayi Sardaunan Sokoto, kuma mata ga marigayi Marafan Sokoto, Ahmad Danbaba, ta rasu tana da shekaru 76 a duniya bayan doguwar rashin lafiya.
Marigayiyar, ta rasu a wani asibiti dake Hadaddiyar Daular Larabawa (Dubai), kamar yadda danta, Hassan Danbaba ya sanar.
Yanzu haka, an fara shirye-shiryen dawo da gawarta gida Najeriya don yi mata sutura kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.
Ta rasu ta bar ‘ya’ya biyar, daga cikinsu akwai Magajin garin Sokoto, Hassan Danbaba da Asma’u, mata ga Sarkin Sudan Shehu Malami da Hadiza da Uwani sai ‘yar autarsu Aisha da jikoki 26.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *