Yar wasan Hausa Hafsat Idris wadda aka fi sani da Ɓarauniya ta mallaki tsaleliyar mota.

Ta sanya motar ne a turakarta ta facebook tana faɗin a taya ni murna.

Hafsa Idris a kwanan baya ne ta aurar da ɗiyarta aka yi shagalin buki na ji da faɗi in da ‘yan uwanta masu harkar wasan Hausa suka yi mata kara.

Har in jiki ne ta ji ba ta gama murmurewa ba sai ga maganar tsaleliyar mota ta ji da faɗi ita ma  Marsidiz benz ta mallaka.

Duk da dai Hafsat ba ta yi bayani ba a yanzu yanda ta mallaki motar, saya ta yi ko kyauta aka ba ta, kawai dai ta nuna yanzu motar mallakinta ce.

Hafsat tana cikin mata masu shirya fim da ke da abin hannunsu wanda ke bayyanawa ƙarara ta hanyoyin kafar sada zumunta, musamman irin yanda suke holewa da kuɗin a tafiye tafiye da mallakar kayan alfarma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *