Spread the love

Daga Gimbiya  Amrah

Kayan haɗi:
Chicken wings (fiffiken kaza ki yanka shi pieces)
Spices of your choice
Seasoning
Hot sauce (I used homemade)
Ketchup
Chili sauce
Dark soy sauce
Brown sugar/ honey
Butter

Yanda za ki samar da girkin:

Ki wanke wings, ki hade spices da seasoning a wuri guda, sai ki zuba a kan wings din ki murza sosai da hannunki yanda zai shiga ciki. Sai ki rufe da cling film ki saka a fridge ya yi 5 hours.
Bayan awa biyar sai ki ciro, ki shimfida baking paper a kan oven tray ki jera wings din a kai, ki saka a oven ki gasa har sai ya gasu.

Sai ki ciro, ki zuba hot sauce a pan, ki zuba brown sugar/zuma, ki zuba ketchup, soy sauce, da chili sauce ki yita juyawa har sai kin ga ya yi kauri. Sai ki zuba butter ki barshi ya yi melting sannan ki zuba gasasshen wings din a ciki ki yita juyawa. Idan ya game ko’ina sai ki sauke.

Wannan nau’in girkin kenan, mai karatu in kana buƙatar ƙarin bayani kan girkin da sauran abubuwan da suka shafi girkin mata kana iya tuntuɓar Managarciya domin haɗa da mutanen da suka da ce da muradinka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *