Spread the love

Daga Muhammad M.Nasir.

Tsohon Gwamnan Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa jigo ne a jam’iyar PDP a jiha da kasa baki daya, ya jagorancin jihar Sakkwato tsawon shekara takwas tun daga 1999 zuwa 2007.

Gwamnatin Bafarawa wata gwamnati ce da mutanen jiha suka amfana da ɗimnbin aiyukkan more rayuwa a birane da karkara har zuwa yanzu ana cin gajiyar ɗimbin aiyukkan da ya aiwatar a jiha.

Mulkin Bafarwa ƙwaran gaske talakawa musamman a karkara sun amfana ‘yan kasuwa da masu harkar kwangila da ‘yan siyasa duka sun more, amma a gefen ma’aikatan gwamnatin jiha kam babu sam barka domin ba wata walwala da suka samu saman albashinsu da ake biyansu kan kari, haka masu karɓar fansho da garatitu ba su iya tuna gwamnatinsa su yi farinciki da ita.

Bayan Bafarawa ya kammala wa’adinsa tare da barin dimbin abin da ba za a iya mantawa da shi ba, kamar samar da gidaje 500 da gina gadar sama da samar da makarantar hardar Kur’ani da gina hanyar Sakkwato zuwa Silame da Binji da Tangaza da Gudu da gina hanyar Kware zuwa Gada da Sakkwato zuwa Sabon Bini da Isa da sauransu, sai ya dauki halin ƙauracewa Sakkwatawa ba a ganinsa a cikin kowace hidima a jihar, abin wasu ke danganta hakan da baƙar adawar da ke tsakaninsa ne da wanda ya gade sa tun da ba’a son ransa ya zauna in da ya tashi ba.

Bafarawa ya cigaba da jan zaren siyasarsa a gefen adawa in da yakan zo a yi siyasa bayan zaɓe ya tafi abinsa ba tare da ganin shi cikin hidimomin al’umma ba, har zuwa lokacin da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya sauya sheƙa zuwa PDP, anan ne ya dawo tare da gwamnati.

Haɗuwar Bafarawa da Tambuwal ya sauya abubuwa da dama a cikin tafiyar siyasarsa da zamantakwarsa da al’ummar gari abin da ake kallon  ko Bafarwa yana son sauya siyasarsa ne ko kuma ya  yi da ya sanin abubuwan da suka faru a baya.

Bafarawa a tafiyarsa da Tambuwal ya so a biya masa buƙatar faɗin abin da Tambuwal ya gada ga gwamnatin Wamakko domin Sakkwatawa su san wane ne masoyinsu a tsakanin shi da Wamakko, akwai hanya a ƙaramar hukumar Gudu da Gada da Gadar garinsu ta kwashe ya so a ɗauki harama amma dai har yanzu shiru abu ne kawai da Allah ya sani ‘karatun Kurma’ waɗannan buƙatun ba su biya ba.

Bafarawa ya jingine adawarsa da Wamakko sun koma mutane masu mutunta juna, abin da ake kallo da hasashen suna iya siyasa ɗaya a 2023 in damar hakan ta bayar domin a yanzu magoya bayansu sun daina kallon kallo da neman samun sa’ar juna domin musgunawa da walakantawa.

Alamu ya nuna Bafarawa ya fara dawowa daga rakkiyar tafiyar Tambuwal ganin yanda a tafiyar ya zama ɗan kallo a tsarin tafiyar da jam’iya da gwamnati wanda hakan nada nasaba da shirun da aka ji ga talakawan da ya ɗaukarwa alƙawalin kammala masu wasu aiyukkan cigaba in har gwamnatin Tambuwal ta sake dawowa.

A yanzu Bafarawa yakan tafi hidimar jama’a da jawo su a jiki in da a wannan watan na Ramadan ya shirya buɗa baki da su, abin da ba a gani ya yi ba shekara 20 da suka wuce.

Managarciya na hasashen Bafarawa na yunƙurin tayar da gidan siyasarsa ya dawo da tasirin da ana iya haɗaka da shi a siyasar gaba domin samar da nasara hakan ke nuna yana yunƙurin sauya siyasar Sakkwato domin ta hau turba da ta dace da za a iya kawo cigaba musamma a cika alƙawalin da aka ɗaukarwa mutane a lokacin yaƙin neman zaɓe a 2019.

Kashe wutar adawa a tsakaninsa da tsohon mataimakinsa Sanata Wamakko hoɓɓasa ce da za ta sauya siyasar jiha da za a iya samun cigaba a cikin al’umma da kanta jihar.

Yanda Bafarawa ya ɗauko wannan tafiyar lalle shiri ne na sauya siyasar jihar  wanda za ta kasance cikin lumana da goyon bayan wanda mutane ke so domin ba ɓangaren da ake baƙar adawa da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *