Spread the love

Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya roki Gwamnan Babban Bankin Kasa(CBN) Mista Godwin Emefiele da ya dakatar da shirinsa na fara cire kudin bashin da aka rantawa jihohi domin halin da ake ciki na rashin tsaro.

Tambuwal ya shiga cikin maganar da gwamnan ya yi na cewa jihohi su fara dawo da kudin bashin da aka ba su ga babban banki ko duk abin da ya same su; su ne suka ja.

Tambuwal haka kuma ya yi kira ga Ministar Kudi Zainab Ahmad ta roki gwamnan Banki da ya jingine batun sanya kafar wando daya da jihohi kan rancen saboda akan tsaro ne aka bayar da bashin kuma har yanzu matsalar tsaron tana nan karuwa ma ta yi.

“Idan jihohi suka fara biyan bashin da aka ba su tau a ina za su samu kudin da  za su tabbatar da tsaron makarantun da ke karkashinsu?” Tambayar da Tambuwal ya yi.

Gwamna Tambuwal ya sanar da daukar matakan da suka yi domin kare dalibban makaranta da malamansu a jihar Sakkwato.

Gwamna ya yi kalaman ne a Abuja ranar Talata a wurin taron da ya shafi samar da  kudi domin tallafawa makarantu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *