Spread the love

 

 

Alhaji Ali Sarkin Mota wanda yake shi ne babban direban Sardaunan Sakkwato Ahmadu Bello ya rasu, kamar yadda  iyalan Sarkin Motar suka  tabbatar da rasuwarsa a safiyar Laraba, bayan fama da rashin lafiya.

 

Sun sanar  za a yi jana’izarsa bayan Sallar Azahar a Babban Masallacin Sultan Bello da ke Unguwar Sarki, Kaduna.

 

Marigayin na daga cikin daidaikun makusantan Sardaunan da a gban idonsu sojoji suka yi wa Sardauna juyin mulki tare da  kashe shi a shekarar 1966.

A wata hirar da Aminiya ta yi da shi a lokacin rayuwarsa, marigayin ya bayyana mata tun daga yadda sojoji suka kutsa a cikin gidan Sardaunan cikin taskar dare, suna barin wuta, har suka kashe shi tare da mai daikinsa.

Bayan tuka ubangidansa Sardauna wanda ya nada shi Sarkin Mota, Alhaji Ali ya kuma tuka Sarauniyar Ingila da shugabannin kasashen duniya da dama da suka ziyarci Najeriya a zamanin Sardauna.

Marigayi Ali Sarkin mota ya rasu ya bar ’ya’ya da jikoki da dama, kuma ya kasance abin girmamawa ga makwabta da dattawan Arewa.

Managarciya na yin ta’aziya ga iyalai da abokai da masoyan margayin kan rashinsa da suka yi.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *