Spread the love

Majalisar zartarwa ta kasa wadda shugaba Buhari ke jagoranta ta aminta da fitar da kudi biliyan 8.39 a zubawa hanyar da ta taso daga Sakkwato zuwa Tambuwal zuwa Jega zuwa Makera.

Ministan aiyukka da gidaje Babatunde Fashola ya fitar da bayanin a ranar Laraba a lokacin da yake yi wa manema labaran fadar shugaban kasa bayani jim kadan da kammala taron majalisar wadda Buharin ya jagoranta da kansa.

Fashola ya ce kara zubawa aikin hanyar kudin  ya zama dole domin canjin kayan aiki da aka samu a hanyar mai nisan kilo mita 185 da aka baiwa kamfanin CRCC.

Ya ce kamfanin ya nemi a kara masa kudi biliyan 8.39 abin da majalisa ta aminta da shi kenan saboda canjin kaya da aka samu, an bayar da aikin a tsakanin shekarar 2012  tun sanda aka ba da aikin zuwa yanzu akwai kilomita 85 da ke son a sake gyarawa da gina sabuwa ganin shekara 12 da ba da aikin wasu wuraren ya lalace.

Ya ce hanyar tana da kashi biyu ne daga Sakkwato zuwa Makera kashin farko da aka baiwa kamfanin Triacta kilomita 296 ne an kammala su kwanannan motoci na hawansu. A kashi na biyu da yake da kusan kilomita 100 Yawuri zuwa Makera su ne za a zubawa kudin domin kammalawa in da muke da kilo mita 85 da za a yi aikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *