Spread the love
An kashe shugaban ƙasar Chadi Idriss Deby!
Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya rasu a wannan Talata ‘yan sa’o’i bayan da aka bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a baya-bayan nan. Rundunar sojin kasar ta Chadi ce ta sanar da mutuwar shugaban, inda ake zullimin ya mutu ne a sanadiyyar raunin da ya samu a “fagen daga” wurin  yaki da  ‘yan tawayen da ke hankoron kwace iko da gwamnatin kasar.
Shugaban ya daɗe saman mulkin ƙasar a lokacin rayuwarsa ya yi ƙoƙari sosai wajen ganin ta samu zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *