Spread the love

 

Amarya ta nemi kotun shari’ar musulunci dake zamanta a Samaru Gusau jihar Zamfara ta raba aurenta da sabon angonta da aka ɗaura masu aure sati ɗaya da ya wuce kan wahalar da take sha a wurin saduwa da ita.

Aisha Ɗan Nufawa bazawara ce da ta haifi yara uku a wajen mijinta na farko kafin aurenta ya mutu ta auri wannan.

A bayaninta ta ce a al’ada in aka yi auren bazawara tana tafiya kakkaɓar gara wanda haka na iya sanya saduwa da mijin, a lokacin da mijin ya sadu da ita ta ɗauka za ta ji daɗi ne amma sai wani abu ya faru daban na wahala saboda al’urarsa tana da girma sosai. Kamar yadda ta shedawa kotu.

Ɗan Nufawa ta ce angon ya ji mata ciwo a karon farko da ya sadu da ita haka a na biyun sai da mahaifiyarta ta taimaka mata da maganin gida, a haka ta ga gaskiya ba za ta iya cigaba da auren ba saboda girman al’urar angon.

Mijin a gaban kotu ya aminta da duk abin da matar ta faɗi amma abin da take nema na rabuwar ya aiwatar da haka tun sati ɗaya da ya wuce ya sake ta.

Hakan ke nuna tun kafin kotu ta raba auren shi mijin ya yi saki da kansa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *