Spread the love

 

Daga Muhammad M. Nasir.

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko jigo ne a jam’iyar APC ya yi kira ga magoya bayan jam’iyarsu musamman a jihar Sakkwato da su roki Allah ya isar musu ga wadan da suka zalunce su a zaben gwamna da aka yi  a shekarar 2019 a cikin wannan watan na

Ramadan da yake da dimbin falala da gafarar Allah.

Sanata Wamako da yake wakiltar Sakkwato ta Arewa a majalisar dattijan Nijeriya ya furta kalaman ne jim kadan bayan ya dawo gida daga birnin Abuja ya ce akwai bukatar magoya bayan, su cigaba da rokon Allah ya isar musu ga duk wanda ya sa hannu aka yi masu magudin zaben a 2019 wanda kowa yasan an zalunce su.

Zaben gwamna da gudanar tsakanin gwamna Aminu waziri Tambuwal na PDP da Ahmed Aliyu na APC, gwamna Tambuwal ya samu nasarar lashe zaben da kuri’u 342 kamar yadda hukumar zabe ta bayyana yawan kuri’un da kowannensu ya samu.

Jam’iyar APC da dan takararta sun kalubalanci ingancin zaben zaben Tambuwal a gaban kotu a karo uku amma dukan kotunan sun tabbatarwa Tambuwal nasara.

Magoya bayan jam’iyar APC sun zargi akwai zalunci da nuna karfi a cikin lamarin don haka ne jigon tafiyar wanda yake tsohon gwamna ne a Sakkwato  ya kara rokonsu da ka da su karaya su cigaba da rokon Allah ya isa kan zaluncin da aka yi masu.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *