Kungiyar shugabannin kananan hukumomin Sakkwato wadda aka fi sani da ALGON sun zabi shugabanninsu da za su ja ragamar kungiyar har karshen wa’adin mulkinsu.

Kungiyar ta zabi Alhaji Mustapa Shehu wanda yake shugaban karamar hukumar Sakkwato ta Arewa ne a matsayin Shugaban ALGON na Jiha.

Sabon shugaban ana da yakini kansa na zai kwatanta a jagorancin da zai yi domin an san shi da mutunta abokan hulda da karbar shawara domin samun cigaba a in da aka sanya shi jagoranci.

Alhaji Aminu Aya Gwadabawa daga Gwadabawa a matsayin Mataimakin Shugaba, sai Alhaji Lawali Fakku daga Kebbe a Matsayin Sakatare, in da aka zabi shugaban karamar hukumar Illela jami’in hulda da jama’a na kungiyar.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *