Spread the love

 

Daga Muhammad M. Nasir.

Matsalar karancin ruwan sha da ta dabaibayi birnin Sakkwato da kewaye al’ummar cikin birnin na fama da wahalar neman ruwan domin amfanin yau da kullum kan haka Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya ba da tasa gudunmuwa don rage wahalar da ake ciki.

Raba ruwan da Sanata Wamakko ya  yi musamman a cikin wannan watan na Ramadan zai kara kawo sauki a cikin al’umma ganin yanda suke ta fadi tashin neman ruwan ba dare ba rana.

Matsalar karancin ruwan sha a jihar Sakkwato ta kusan wata biyu musamman yanda ta’azara a unguwar Minanata, Runjin Sambo, Gidan dare da wasu wurare a kwaryar Sakkwato.

Sanata a ranar Alhamis data gabata ya ba da umarnin raba ruwan a unguwar Kofar Taramniya da Kofar Atiku da Majema da Gidan Haki da Unguwar Malamai da Assada da Masallacin Shehu da Majema da Kan titin Manuri.

Wannan yunkurin abin yabawa ne musamman yanda ya sa a kai ruwan a wasu masallatan Jumu’a domin amfanin masallata.

A wani rubutu da aka yada a kafofin sada zumunta wanda aka nuna kwamishinan ruwa ne na jihar Sakkwato Alhaji Umar Bature ne ya rubuta ya tabbatar da matsalar sai dai bai bayyana lokacin da za su shawo kan matsalar  ba.

“Muhimmin abin da ya dace al’umma su yarda da shi akan haka shi ne, kalubalen dake da matsalar samar da ruwa a Sokoto tana da yawa, amma duk da haka mun shawo kan mafi rinjayen ta; don inganta samar da issasun ruwan sha da kuma magance hakan a nan gaba ga al’ummar mu.

“Aikin gina hanyoyin da sake fasalin gina magudanun ruwa a wasu wurare dake birnin Sokoto sun taimaka matuka ga matsalar tare da karancin lantarki da matsala canjin yanayi dake akwai a yanzu a wannan yankin namu.

“Ma’aikatar ruwa da albarkatunsu za ta ci gaba da fitar da bayanai ga dukkan hanyoyin da suka dace, ganin al’umma ba su kara fuskantar matsala akan samar da ruwan sha a wannan jaha ba.” Kalaman Kwamishina.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *