Bayan kashe Mutum 9 da sace shanu 500 Tambuwal ya jajantawa mutanen Rarah

 

A ranar Litinin ta satin da ya gabata ne mahara dauke da bindigogi saman babura sun kai  200  suka afkawa garin Rarah cikin karamar hukumar Rabah a jihar Sakkeato in da suka kashe mutum 9 suka tafi da shanu 500.

Maharan sun shigo cikiin garin ne da rana tsaka suka rika harbi kan mai uwa da wabi har suka samu nasarar aika-aikar da suka zo yi, sun raunata mutane da dama ciki har da wata tsohuwa da aka sanya harsashe a bakinta aka farke fatar bakinta tana a asibiti domin karbar magani.

Gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ya kai gaisuwar jajantawa ga mutanen garin a jiya Jumu’a ya nuna damuwarsa kan lamarin ya yi kira al’umma su rika bayar da bayani ga jami’an tsaro ga wadan nan hare-haren da ke faruwa.

Gwamnan ya umarci shugaban karamar hukuma ya rika taron majalisar tsaro domin daukar matakan da suka dace tsakanin jami’an tsaro da gwamnatin jiha.

Ya ce bai kamata mahara kusan 200 su zo saman babura da rana tsaka su yi harbe-harben kan mai uwa da wabi su sace dabbobi bayan sun kashe mutane su tafiyarsu, a kasa samun mutun daya daga nan da zai jawo hankalin  gwamnatin jiha da jami’an tsaro, akwai bukatar yin abin da yakamata domin gaba.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *